Monday, May 5
Shadow

Jihar Kebbi ta gano karin ma’adanan karkashin kasa a jihar

Jihar Kebbi ta gabo karin ma’adanai na karkashin kasa a jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Yakubu Ahmed-BK ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Yace an gano karin ma’adanan ne a Jega, Dandi, Gwandu, Suru, Birnin Kebbi, Argungu da sauransu.

Wannan na zuwane a yayin da jihar Kebbi ke da ma’adanai kamar su gwal da sauransu.

Ya bayyana gano wadannan karin ma’adanai da cewa, wata hanyace ta karin samun kudin shiga ga jihar.

Karanta Wannan  Kalli Sojan Najeriya, Abubakar Affan da ya ajiye aiki ya shiga aikin sojan kasar Rasha dan ya tayasu yaki da Ukraiynee, yace yana bukatar Addu'ar ku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *