
Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa, Jimullar Naira Tiriliyan 2.23 ‘yan Najeriya suka biya a matsayin kudin fansa ga ‘yan Bindigar daji.
Hukumar tace an biya wadannan kudadene a tsakanin shekarun 2023 zuwa 2024.
Hakanan bayanan sun ce an yi garkuwa da mutane sau Miliyan 2.2 a tsakanin wannan lokaci.
Sannan a kalla kowane mutum an biya mai Naira Miliyan 2.7 a matsayin kudin fansarsa.