Shugaban Gwamnonin jam’iyyar PDP, kuma Gwmana jihar Bauchi Bala a Muhammad ya gargadi Shugaban ƙasa cewa kada ya nuna ģìŕman kai, ya kuma saurari ra’ayin al’umma akan illolin haraji.
Gwamna yana mai jaddada cewa, idan aka amince da dokokin haraji da aka gabatar, hakan zai iya haifar da barazana ga ci gaban ƙananan hukumomi da jihohi.
Mohammed ya soki matsayin Tinubu kan dokokin harajin da ya kira “ba na dimokuradiyya ba,” yana cewa ko wadanda suke mulkin soja za su saurari al’umma kuma su magance matsalolinsu.
Kaura ya yi suka ga dokokin harajin Tinubu a gaban Majalisar Ƙasa, yana mai cewa an tsara su ne don fifita wata yanki fiye da wata.