
A yayin da dangantaka ke kara tsami tsakanin shugabancin Izala na kasa da Izalar Jos.
A baya Sheikh Dr. Musa Salihu Alburham ya soki Sheikh Nura Khalid wanda aka fi sani da Digital Imam inda har ‘ya’yan malam suka mayar da martani.
A yanzu kuma fadan ya kara fadada inda Wani daga cikin Malaman Izalar Jos ya fito ya zargi shugabancin Izala na kasa karkashin Jagorancin Sheikh Bala Lau da zalintar marayu.
A baya dai an samu rashin jituwa tsakanin Izalar Jos data Kaduna wadda daga baya aka zo aka sasantasu.