
Wata Kungiyar Yarbawa me suna Ìgbìnmó Májékóbájé Ilé-Yorùbá ta bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gaza a fannin inganta tattalin arziki da samar da tsaro.
Kungiyar a sanarwar data fita daga bakin shugaban ta, Olusola Badero wanda me magana da yawunta, Princess Balogun ya fitar.
Yace Talauci musamman a yankin Yarbawa ya karu hakanan matsalar tsaro ta karu.
Ya kawo misalin cewa kwanannan aka sace wasu manoma a yankin inda sai da danginsu suka tara kudi sannan aka sakesu.
Yace Tinubu ya kasa cika Alkawuran da ya dauka, dan haka yace Aso Rock ba gidan gado bane, kada ma Tinubu yayi tunanin tsayawa takara a 2027 dan ba ci zai yi ba.