Kafar mu kafar Kwankwaso a siyasa – Abba Gida Gida

Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya sake jaddada kudurinsa na mara wa Sanata Rabiu Kwankwaso baya a dukkan harkokin siyasa.
Gwamna Yusuf ya sha alwashin bin tafarkin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa, “duk inda ya dosa a siyasa, magoya bayansa za su bishi.”
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga kansiloli 484 daga kananan hukumomi 44 a fadar gwamnati ranar Lahadi.
Abba ya kuma karyata zarge-zargen da tsohon sakataren gwamnatin jiha, Baffa Bichi, ya yi masa, inda ya kira shi da “makaryaci marar kunya,” yana mai bayyana zarge-zargen a matsayin karya kuma abin dariya.
Gwamnan ya fi mayar da hankali kan zargin cewa Kwankwaso na karɓar Naira biliyan biyu duk wata daga gwamnatin jihar Kano, yana mai cewa wannan zargi ne mafi girman rashin gaskiya da siyasar son rai.
Gwamman ya yabawa Kwankwaso a matsayin “daya daga cikin mutanen da suka fi tsarkin zuciya da sadaukarwa a Kano,” yana mai cewa bai taɓa neman kuɗi daga gwamnati ko tsoma baki cikin harkokin kuɗin gwamnati ba.
Gwamnan ya tambayi dalilin da yasa Bichi bai bayyana irin wannan zargi tun yana kan mulki ba, yana mai cewa ya yi shekara fiye da ɗaya a cikin gwamnati ba tare da nuna wata damuwa ba, ya kara da cewa, “yana magana ne kawai bayan da aka kore shi saboda gazawa.”