Sunday, March 16
Shadow

Kai da kace idan ka zama shugaban kasa zaka halasta shan Wìwì shine kake da bakin cewa musulmai Jahilai? Kaine babban dakiki>>Reno Omokri ya mayarwa Sowore martani

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya mayarwa da dan takarar shugaban kasa, kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore martani kan zagin da yawa gwamnonin Arewa saboda sun bayar da hutun makaranta saboda zuwan watan Ramadan.

Sowore yace Gwamnonin jihohin Kebbi, Katsina, Bauchi da kano dakikai ne kuma sakarkarune saboda sun bayar da hutun makaranta dalilin zuwan watan Azumin Ramadana.

Inda ya bayar da hujjar cewa ko Saudi Arabia bata kulle makarantu saboda zuwan Azumin watan Ramadana.

Saidai a martanin da yayi masa, Reno Omokri yace Sowore babban wanda ya jahilci kundin tsarin mulkin Najeriya dan kuwa kundin tsarin mulki yace kula da makarantun Primary dana Sakandare yana karkashin ikon gwamnatocin jihohi ne.

Karanta Wannan  Miji ya saki matarshi bayan da mawakin Amurka, Chris Brown ya sumbaceta

Yace idan kuwa kamar yanda yake cewa idan ya zama shugaban kasa zai hana bayar da irin wannan hutu, yace to saidai idan zai take doka ne yayi hakan.

Reno yace kuma Saudi Arabia da ya bayar da misali da ita, a baya tana bada hutu saboda zuwan watan Ramadan amma yanzu an canja tsarin inda aka baiwa kowane yanki na kasar damar yanke hukuncin amincewa ya bayar da hutun makaranta a lokacin azumin watan Ramadana ko kuwa a’a

Yace dama yake wannan maganar, shifa Sowore ne yace idan ya zama shugaban kasa zai halasta shan wiwi, yace shine kuma yake magana dan an bayar da hutun makaranta, yace kuma yana ina ‘yan IPOB ke kulle makarantu duk ranar Litinin, bai yi Allah wadai da wancan ba sai wannan da aka kulle na tsawon sati 4 kawai saboda yin ibada?

Karanta Wannan  Gwamnoni sun kai ziyarar jaje zuwa Maiduguri

Yace kuma yaya Sowore yake ganin zata kaya tsakaninshi da mutanen da yake son su zabeshi ya zama shugaban kasa alhalin yanzu yana zaginsu?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *