Wednesday, October 9
Shadow

IMF ya nemi Tinubu ya tausaya wa talakawan Najeriya

A daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a kan ƙarin farashin man fetur, Asusun Lamuni na Duniya, IMF, ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ba ɓangaren rage wa talakawan ƙasar raɗaɗi muhimmanci.

Da yake jawabi a tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise TV a jiya, babban wakilin IMF a Najeriya, Dokta Christian Ebeke ya ce har yanzu ba a kai farashin man fetur ɗin asalin farashinsa na kasuwa ba, wanda hakan ke nuna cewa za a ƙara farashin a nan gaba kamar yadda jaridar Vanguard ta kalato.

Idan ba a manta ba, shi ma kamfanin NNPCL na Najeriya ya bayyana irin wannan matsayar a baya.

Babban jami’in na IMF ya bayyana damuwarsa a kan irin wahalar da ƴan Najeriya suke ciki a sanadiyar wasu matakai da gwamnatin ƙasar ta ɗauka.

Karanta Wannan  Duk da kisan da akawa mutane a jiharsa, Gwamnan Yobe,Mai Mala Buni yana gidansa dake Abuja bai koma jihar tasa ba

A cewar Ebeke, “Ina tunanin ƙarin farashin man ya zo ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cikin tsananin rayuwa.

“Ƴan Najeriya suna fama da matsaloli da dama kamar hauhawar farashin kayayyaki kamar su abinci ga ambaliya da sauransu.

“Don haka ƙara farashin man sai ya zo a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ke tangal-tangal, kuma ƴan Najeriya ke cikin tsananin rayuwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *