
Hukumar ‘yansandan jihar Oyo sun sanar da kama wasu mutane da suka kware wajan tono gawar matattu bayan an binnesu a makabarta dan yin sihiri.
A sanarwar data fitar ranar Talata, 18 ga watan Maris, Hukumar ‘yansandan jihar tace ta kai samame gidan wani mutum me suna Ridwan Bello dan shekaru 35 bayan samun bayanan sirri akansa.
Tace kuma ta yi sa’a ta iske gangar jikin wata mata babu kai babu kafafu da kasusuwan mutane. Mutumin wanda wasu lokutan ana kiransa da sunan Asalailu ya bayyana amsa laifinsa.
Yace yana kaiwa wani matsafine sassan jikin yana saye.
Ridwan ya kai ‘yansandan har kabarin da ya tono gawar.
Sannan ya kaisu gurin mutumin da yake sayarwa da sassan jikin wani me suna Fatai Adeleke dan kimanin shekaru 70.
Shima ya amsa laifinsa.
Hukumar tace an kaisu bangaren binciken masu kisan kai sannan ana kokarin kama sauran masu hannu a lamarin.