
Hukumar ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja ta kama wasu mata 2 ‘yan uwan juna bisa shirya garkuwa da daya daga cikinsu dan su damfari mahaifinsu Naira Miliyan 5.
Mahaifin nasu me suna Mr. Innocent ne da kansa ya kai karar bacewar diyarsa, Miss Leadway Innocent ‘yar Kimanin shekaru 16 wadda yace tun da ta tafi rubuta jarabawa a Government Secondary School, Karu bata koma gida ba.
Ya kai karar ne ranar 30 ga watan Yuli 2025 inda yace tun ranar 18 ga watan na Yuli diyar tasa ta bace.
Kakakin ‘Yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace mahaifin ya kai korafinne a ofishin ‘yansanda dake Jikwoyi Division.
Yace daga baya an kirashi inda aka ce an yi garkuwa da diyar tasa ne ana neman ya biya kudin fansa.
Tace hukumar ‘yansanda ta bazama bincike inda ta gano diyar mutumin a tare da wasu miji da mata suna sha’aninsu babu wata alamar cewa, an yi garkuwa da itane.
Ci gaba da Bincike yasa an kamo yayar wadda aka sace din me suna Miss Joy Innocent da Saurayinta me suna Mr. Mayowa Adedeji.
Da bincike yayi tsanani an gano Joy Innocent ce ta shirya yin garkuwar karya da kanwarta, LeadWay bisa hadin bakin saurayinta Mayowa Adedeji dan su karbi kudi a hannun mahaifinsu.
Sannan ita kanta LeadWay ta san da wannan shiri har ma tana taimakawa dan ya tabbata.
Duka su hudun suna hannun ‘yansanda kuma sun amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
Nan gaba dai za’a gurfanar dasu a gaban kotu dan zartas musu da hukunci.
Kwamishinan ‘yansandan Abuja, CP Ajao Saka Adewale yayi Allah wadai da wannan abu inda yayi kira ga mutane dasu rika kula da halayyar ‘ya’yansu.