Friday, January 16
Shadow

Kai ka taba cewa shekaru 4 sun yi kadan shugaba ya kawo canji a Najeriya amma gashi yanzu kana sukata>>Shugaba Tinubu ga El-Rufai

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayar da martani ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kan sukar da ya masa a gidan talabijin na Channels TV.

Shugaban ya mayar da martanin ne ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga ta kafar X.

Ya rubuta cewa a shekarun baya, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yace shekaru 4 sun yiwa shugaban kasa kada ya gyara Najeriya ko ya kawo ci gaba amma yanzu yana sukarsa.

Yace amma duk da haka ya kawo abubuwan ci gaba Najeriya sosai.

Misali an samu habakar arziki sosai ta bangaren kasuwar hannun jari inda aka samu karuwar dukiya data kai naira Tiriliyan 26.

Karanta Wannan  Bayan da ta zargeni da nemanta da lalata Har Hotunan Selfie Sanata Natasha Akpoti ke daukar mu ni da ita idan mun tafi aiki, saboda tsabar jin dadin aiki dani kuma nace ta kawo hujjar zargin da take min amma taki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *