Monday, March 24
Shadow

Idan kuka sake kuka kkasheni zaku dandana kudarku>>Trum ya gayawa Iran

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gargadi kasar Iran da cewa idan suka sake suka kasheshi zasu dandana kudarsu.

A baya dai lokacin Trump yana yakin neman zabe an kaiwa Trump hari inda aka so kasheshi saidai ya tsallake rijiya da baya inda kuma aka zargi cewa kasar Iran ce ta kai masa harin.

Saidai tuni kasar Iran ta fito ta karyata wannan zargin da ake mata inda tace ba itace ta kaiwa Trump hari ba.

Wasu masu sharhi kan al’amuran yau da kullun sun bayyana cewa, watakila kasar ta Amurka na wannan maganane saboda kawai tana son fara yakin kai tsaye da kasar Iran.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda matar aure ke lakadawa mijinta duka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *