Kakanninmu asali ƴan Najeriya ne – Shugabar Majalisar Dattawan Saint Lucia ta shaida wa Tinubu.

Shugabar Majalisar Dattawan kasar Saint Lucia, Alvina Reynolds, ta bayyana karfin alaƙa ta asali tun kakanni tsakanin ƙasar da Najeriya.
Reynolds ta buga misali da bayanan ƙidayar al’umma na Biritaniya da aka gudanar a tsibirin a 1815, inda aka gano cewa yawancin mutanen Saint Lucia na da asali daga Najeriya.
Ta bayyana hakan ne yayin tarbar Shugaba Bola Tinubu a zama na hadin gwiwa na majalisun dokoki biyu na kasar Saint Lucia a jiya Litinin.
Bayani game da wannan zaman hadin gwiwa, ta fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar ga manema labarai a jiya Litinin a birnin Abuja.
“Daga cikin bayi 16,282 da aka kawo Saint Lucia a waccan shekarar, 3,488 an haife su ne a nahiyar Afrika.”
“Daga cikin wannan adadi, kashi 34 cikin 100 sun fito daga Najeriya, kashi 11 kuma daga Najeriya-Kamaru, sai kuma kashi 22 daga yankin Congo.”
“Sauran 12,794 an haife su ne a Saint Lucia, amma yawancin kakanninsu sun fito ne daga yankin Sene-Gambia da Najeriya,” in ji ta