Tuesday, December 3
Shadow

Kalaman soyayya masu sanyi

Ilahirin Lokaci Mai Zuwa Cikin Jiran Tsammani Mazubin Abinda Zuciya Ta Kunsa Sun Lamunci Zuciya Wajen Himmatuwar Ruhi Cikin Wakiltar Lokaci Wajen Iso Da Sakon Gaisuwar Aminci Agareki

Yake Wannan Kyakkyawa Hakika Banzo Akan Lokacinda Yakamata Ace Nazo Ba Saidai Ban Cire Tsammanin Samun Wani Kaso Daga Cikin Bangaren Zuciyarki Ba

Tabbas Mallakar Zuciyar Mace Kyakkyawa Mai Tsananin Aji Irinki Babban Aikine, Amma Hakan Baisa Na Cire Tsammani Ba Domin Ance Rabon Mutum Baya Wuceshi

Nazo Ne Da Dukkan Karfina Wajen Tunkarar Gagarumin Yakin Dake Gabana Wajen Gwabzawa Da Dukkan Wani Mahalukin Da Zai Iya Hanani Karasowa Cikin Fadar Zuciyarki

Karanta Wannan  Labarin soyayya mai ban dariya

Tabbas Mallakar Zuciyarki Babban Aikine Saidai Nayi Alkawarin Sadaukar Da Dukkan Lokacina Wajen Samar Da Wani Gini Mai Karfin Da Guguwa Bazata Iya Rushewa Ba

Sone Silar Budewar Kofofin Zuciya Dan Allah Karki Zamto Murfin Kofar Da Zai Kulleni Cikin Duniyar Da Bazanga Hasken Murmushin Bakinki Ba

Ke Ta Musamman Ce Acikin Jerin Yan Mata Kinada Muhimmanci Acikin Rayuwata Irin Yanda Bazan Amfani Kaina Ba Matukar Ban Samu Damar Mallakar Zuciyarki Ba

Kin Ciri Tutar Zama Sarauniya Shiyasa Ake Kiranki Da Gimbiya Nikuma Ina Cemiki Habibiya,, Yaya Kallon Ido Zai Kasance Alikacinda Gimbiya Tazamo Sarauniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *