Ga kalaman Yabon Budurwa kamar haka wanda zasu sa ta ji tana sonka sosai:
Nasan dandanon zuma, nasan na suga, nasan na madara na san na mangwaro,nasan na ayaba, nasan na abarba amma har yanzu na kasa gane dandanon soyayyarki saboda kullun jinshi nake sabo a bakina.
Idaniyata.
Ruwan shana.
Zumata.
Idan muka gama tadi na kama hanyar tafiya gida, har sai inje gida a kasa ban sani ba saboda tunanin hirar da muka yi me dadi.
Numfashina.
Budurwata.
Babyna.
Kullun kara burgeni kike.
Wallahi har zuciyata ina sonki.
Ke kadaice.
Idan na rasaki bansan yanda zan yi ba.
Soyayya dake tasa rayuwata ta daidaitu.
Kina da kyau da kwarjini.
Bana gajiya da kallonki.
Na fara jin komai kika yi daidaine.
Bana ganin laifinki ko kadan.
Idan ina tare dake ji nake kamar banda wata matsala a rayuwata.
Danni kadai aka yiki.
Da inada dama dana hana duk wani namiji kallonki.
Ji nake kamar kullun in ta binki ina miki dogari dan kada wani ya cutar min dake.
Ki sace zuciyata, kin cinyeta, kin hadiya.
Bazan daina sonki ba.
Bazan barki ba.
Tatattausan lafazinki yana ratsa duka wata jijiya ta jikina.
Igiyar sonki ta daureni, da kyar nake tafiya.
Yawanci shokin din wutar lantarki aka sani amma akwai shokin din soyayya wanda ke kadai kike saminshi dake gigitani in fita hayyacina.
Dimuwar soyayyarki idan ta kamani har mantawa nake da kaina.
Kanshinki na kwaranye kin duk wani tunanin kunci a rayuwata.
Murmushinki nasa inji dadi a raina marar misaltuwa.
Ina sonki kamar kwai a cokali.
Wani lokacin inason in yabeki amma sai in rasa wace kalma zan yi amfani da ita wadda zata bayyana ainahin abinda nake ji a zuciyata.
Yawancin mutane suna jin waka dan nishadi, wasu su kalli fim,wasu su karanta littafi, wasu su je yawon shakatawa, ni ina samun dukan nishadina idan ina tare dake.