Friday, December 26
Shadow

Kalli Bidiyo: A karshe dai Hisbah ta lalata wajen da aka ce wai an ga Sahun Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a Kano mutane suka rika zuwa suna shan ruwan wajan

Hukumar Hisbah a Kano ta lalata wajan da aka rika yada rade-radin cewa wai an ga sahun Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a Kano.

Wajan dai yana Dakata ne inda aka ga bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sadarwa mutane suna rububin sha da wanka da ruwan wajan.

Mataimakin kwamandan Hisbah na jihar Kano, Muhahideen Aminudeen ya bayyana cewa ko da suka ji labari, sun je wajan inda suka ilimantar da mutanen wajen cewa wannan ikirari karyane.

https://twitter.com/bapphah/status/1914187045083247072?t=sxDEREGOf_DmRbxUOoqQFA&s=19

Sun gayawa mutanen cewa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) bai taba zuwa Afrika ba.

Ya jawo hankalin iyaye da su rika baiwa ‘ya’yansu ilimi na Addini dan su rika banbance gaskiya da karya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda hàtsànìyà ta kaure a majalisa aka so a baiwa Hammata Iska saboda gayyatar gwamnan CBN saboda batan Naira Triliyan 11>>Wasu 'yan majalisar sun yadda a gayyaceshi inda wasu suka ce basu yadda ba

Ya kuma bayyana cewa shan irin wannan ruwa ma na da hadari ga lafiyar mutum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *