
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa akwai wanda suka fishi tsabar kudi a Nijeriya.
Yace amma basu saka kansu cikin irin rigimar da ya saka kanshi ba.
Yana magana ne kan gina matatar man fetur dinsa da kuma rikicin da ya kunno kai tsakaninsa da kungiyar NUPENG.
Dangote yace amma dole ne sai an tallafawa gwamnati, yace ba komai ne za’a nade hannu ace wai gwamnati ce zata yi ba.
Yace akwai abubuwan da dole sai mutane masu zaman kansu sun saka hannu, yace amma irin abinda ake masa zai sa mutane su guji zuwa zuba hannun jari a Najeriya.