Friday, August 7
Shadow

Kalli Bidiyo: Akwai wadanda suka fini kudi a Najeriya>>Inji Dangote

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa akwai wanda suka fishi tsabar kudi a Nijeriya.

Yace amma basu saka kansu cikin irin rigimar da ya saka kanshi ba.

Yana magana ne kan gina matatar man fetur dinsa da kuma rikicin da ya kunno kai tsakaninsa da kungiyar NUPENG.

Dangote yace amma dole ne sai an tallafawa gwamnati, yace ba komai ne za’a nade hannu ace wai gwamnati ce zata yi ba.

Yace akwai abubuwan da dole sai mutane masu zaman kansu sun saka hannu, yace amma irin abinda ake masa zai sa mutane su guji zuwa zuba hannun jari a Najeriya.

Karanta Wannan  An bayyana cewa tsohon Shugaban Jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje na ci gaba da samun sauƙi a bayan kwanciya jiɲÿa da ya yi a birnin London na ƙasar Birtaniya kamar yadda aka bayyana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *