
Farfesa Alkasum Abba ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari yana da gaskiya akan kansa.
Yace amma kuma wanda suka masa aiki dake kusa dashi sun rika satar kudin ‘yan Najeriya ba tare da ya iya hanasu ba.
Yace shugabanci ba kawai ace mutum yana da gaskiya ba shikenan dolene ya zamana idan ka aikata ba daidai ba ya rika magana.
Yace a zamanin mulkin Buhari na soja, haka aka rika jefar da kayan sana’a na masu gasa masara da masu tuyar kosai a bakin titi.
Da yawa dai sun ce sun yafewa shugaba Buhari inda wasu kuma suka ce basu yafe ba.