
A yau ne dai Peter Obi ya jewa iyalan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari gaisuwa a gidan marigayin dake Daura.
A jiya an rika cece-kucen cewa, ba’a ga Peter Obi a wajan jana’izar Buhari ba.
Kwatsam yau da safe sai gashi a Daura.
Ya je ya yiwa dan Buhari, Yusuf gaisuwa sannan ya je ya yiwa ‘ya’yan Buhari mata gaisuwa, saidai a lokacin da yakewa ‘ya’yan Buhari matan gaisuwa ne aka ga dukansu auna murmushi.
Masoyan Peter Obi sun fassara hakan da cewa alamace ta ‘ya’yan Buharin suna goyon bayan Peter Obi.