
Dan siyasa, Mahdi Shehu yace an sace kanin Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare.
Ya bayyana hakane a shafinsa na X inda ya wallafa Bidiyon wani mutum da aka gani zagaye da ‘yan Bindiga rike da muggan makamai yana fadar cewa uwarsu daya ubansu daya da Gwamnan jihar Zamfara.
Mahdi dai yayi tambayar cewa shin ko Gwamnan zai biya kudin fansa.
Ko kuwa zai yi sulhu da ‘yan Bindigar?
Babu dai wata sanarwa data tabbatar da cewa wannan mutumin dan uwa ne a wajan Gwamnan jihar Zamfara.