
Bayan da aka hanata shiga, Sanata Natasha Akpoti ta kutsa da karfin tsiya cikin majalisar Dattijai.
Da farko dai Sanata Natasha Akpoti ta je majalisar ne akan motocin ta inda aka tare motocin aka hanasu wucewa.
Tana tarene da magoya bayanta ciki hadda A’isha Yesufu.
Sanata Natasha Akpoti daga baya ta sauka inda ta taka a kafa zuwa cikin majalisar.
Magoya bayan Sanata Natasha Akpoti sun rika ture jami’an tsaron inda suka samarwa Sanata Natasha Akpoti hanya ta taka zuwa cikin majalisar a kafa.
Magoya bayan sun take mata baya suna rera wakokin yabo.
Majalisar dai ta dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6.