
Wani tsohon dansandan Najeriya da yayi ritaya aka bashi Naira Miliyan 2.8 a matsayin kudin Sallama yace ba zai karbaba.
A bidiyonsa da aka gani yana jawabi yace ya shafe shekaru 35 yana aiki amma a bashi Naira Miliyan 2.8 a matsayin kudin sallama, yace wannan cin fuska ne.
Yayi kira ga shugaban ‘yansanda da ya shiga lamarin.