
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Raddah ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda likitoci ke tserewa daga Najeriya suna zuwa kasashen waje aiki.
Gwamnan yace abin takaici shine a baya likitoci mata daga Najeriya basa fita kasashen waje yin aiki amma a yanzu likitoci mata daga Arewa suma sun bi sahu.
Yace irin wadancan kasashe mutanensu ragwayene basa iya karatun aikin Likita shiyasa suke zuwa su baiwa likitocin Najeriya Albashi me tsoka dan su daukesu.
Ya zargi Likitocin da rashin kishin al’ummarsu.
Saidai hakan ya jawowa Gwamnan suka inda wasu ke cewa ba’a kula da hakkokin Likitocin ne sannan ba’a biyansu albashi me kyau shiyasa.