
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa’a ta bayyana cewa, akwai jikakka tsakaninta da Naziru Sarkin Waka inda tace baya biyan bashi.
Ta bayyana hakane bayan da ta caccakeshi da cewa Rarara ya fishi ya hakura.
Rashida tace ita ta hadawa Naziru Sarkin Waka Lefen aurensa na biyu kuma har yanzu bai biyata kudin ba.
Ta bayyana hakane a wani Live data gudanar saidai da yawa sun bayyana mabanbanta ra’ayi akanta.