
Kungiyar Tsaffin Sojojin Najeriya ta nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya sauke Ministan Babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike daga mukamin Minista.
Kungiyar tace Wike na takawa da wulakanta mutane da yawa inda ta nemi ko da ba’a saukeshi ba a canja masa ma’aikata.
Hakan na zuwane bayan da Wike yayi dambarwa da sojan Ruwa, AM. Yerima akan wani fili da akw rigima akanshi a Abuja.