
Malamin Addinin Islama da akewa lakabi da Malam Ibrahim Matayassara ya bayyana cewa Haukane da rashin lissafi dan an ce an ga kwarkwata a jikin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) mutum ya kawo kazanta a ransa.
Ya bayyana cewa kwarkwatar ta musamman ce kuma taje samun Rahama da Albarkar Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ne.
Yace dan haka ‘yan darika da suke tunanin kawo kazanta ga Manzon Allah to ya kamata a kaisu gidan mahaukata.
Lamarin muhawara akan Kwarkwata ya taso ne bayan da Sheikh Lawal Triumph ya karanto hadisin.