Wednesday, April 8
Shadow

Kalli Bidiyo: Mun Gano Najeriya na aiki da qasar Iyràn a munafurce sannan Gwamnatin Najeriya na da hannu kan matsalar tsaro dake faruwa>>Inji Tsohuwar Firaiministar Canada, Goldie Ghamari

Tsohuwar Firaiministar kasar Canada, Goldie Ghamari ta bayyana cewa, sun gano Najeriya na aiki da kasar Iran a munafurce.

Sannan ta zargi Gwamnatin Tarayya da hannu a matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya.

Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita da dan jaridar kasar Ingila, Piers Morgan da ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Yusuf Tuggar Maitama.

Tace A tsarin Najeriya ya kamata idan shugaban kasa ya zama musulmi, mataimakinsa ya zama kirista hakanan idan shugaban kasa kiristane, mataimakinsa zai zama Musulmi.

Tace amma a gwamnatin tinubu babu wakilcin kiristoci inda ta zargi cewa ana muzgunawa Kiristoci.

Karanta Wannan  Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Ta Shiryawa Ɗalibai Masu Nazarin Halayyar Ɗan Adam, Tambayar Jarrabawa Kan Dambarwar Dake Tsakanin Sanata Godswill Akpabio Da Sanata Natasha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *