
An yi bikin ranar ‘yan mazan jiya ta kasar Amurka inda aka tuna yanda Amurka ta yi yaki a yakin Duniya na daya daga biyu.
Saidai wani abin mamaki shine ganin sojojin kasar Amurka basu iya fareti ba. Basa hada kafa su yi faretin, tafiya kawai auke yi.
Da yawa masu sharhi sun ce alamace cewa basu yi atisayen yin faretin dan wannan rana ta musamman ba.
Saidai Wasu masu sharhin na cewa, hakan ta farune saboda sojojin da yawansu ba bangaren fareti suke ba, suna da wasu ayyukan daban da sukw yi a cikin gidan sojan na kasar Amurka.