Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Ni a wajena babu Malamin da na taba ji ya Zhaghi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Aminu J Town

Tauraron Tiktok, Aminu J. Town ya bayyana cewa, shi duk takaddamar da ake yi, bai taba jin wani malami ya zaghi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba.

Yace matsalar ‘yan Izala itace rashin Nuna Ladabi yayin magana akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)

Su kuma ‘yan Darika abu ko da na karyane indai na bajintane aka jingina na Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) sai su tabbatar da shi.

J. Town yace, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba sai an yi karya akan karamarshi ba, duk abinda zaka fada akanshi ya wuce nan.

https://www.tiktok.com/@aminujtown/video/7559332568961649938?_t=ZS-90QTwlfi5Ev&_r=1
Karanta Wannan  Fafaroma da ya mutu yau na ta shan yabo saboda goyon bayan 'yan Luwadi da Madigo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *