
Wannan matashin da Bidiyonsa ke kasa yace abin kunyane Sanata Barau Jibrin ya jawowa Yankin Arewa tashin da yayi suka yi sa’insa da kakakin majalisa, Sanata Godswill Akpabio akan harin da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace zai kawowa Najeriya.
Shi dai sanata Barau yace baya jin tsoron Shugaban Amurka, Donald Trump sannan ya bayyanashi da matsoraci inda yayi kira ga kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio shima ya daina jin tsoron Trump.
Saidai Matashin yace sam abinda sanata Barau Jibrin Maliya yayi bai kyauta ba.
Yace a baya Sanatan bai taba tashi ya nuna damuwa ba kan matsalar tsaron Arewa sai yanzu dan Trump yace zai kawo Khari?