
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa saboda ya kai ya kawo, Rarara ma Makwaucinsa ne a Abuja Asokoro.
Gfresh yace matarsa watansu 8 da aure amma ko sau daya bata taba zuwa gidansu a Yola ba saboda jin dadin zama dashi.
Ya bayyana hakane a matsayin martani ga masu cewa yana muzgunawa matarsa.
An ga rashin jituwa tsakanin Gfresh da matarsa a ‘yan kwanakinnan wanda yasa mutane da yawa damuwa.