
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Gayu ta kasance jaruma ta farko a masana’antar da ta fara bayyana sayen sabuwar wayar iPhone 17 pro.
Wayar dai wadda kamfanin Apple ya sanar da fitowarta a makon da ya gabata itace ake ta magana a gari musamman tsakanin masoya wayoyi.
Farashin wayar ya haura Naira Miliyan 2 inda a wani gurin ma ana samunta akan Naira 2,990,000.
An ga Jaruma Ummi Gayu a wani Bidiyo da ya watsu sosai tana nuna wayar a hannunta.