Kalli Bidiyo: Wannan mutumin yayi ikirarin yin aiki a karkashin Kamfanin Sheikh Bala Lau inda yace an rike masa hakkinsa ba’a biyashi ba
by Auwal Abubakar
Wani mutum ya dauki hankula sosai a kafafen sadarwa bayan da yayi zargin cewa yana aiki ne a wani kamfani dake karkashin shugaban Izala, Sheikh Bala Lau amma ba’a biyashi hakkinsa ba.
Yace wasu daga cikin abokan aikinsa sun gudu saboda babu Albashi a aikin.
Mutum ya bayyana cewa an kaisu aikin tsaron Titin Jirgin kasa ne.