Rahotanni sun bayyana cewa, Mahaukaciyar wutar Daji ta mamaye wasu sassa na kasar Israela dake yaki da Falasdinawa.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan wutar daji itace mafi muni a tarihin kasar.
Kasar ta Israela na neman tallafi daga kasashen Duniya dan shawo kan wannan wuta.
Wutar dajin ta yi muni sosai ta yanda saida aka soke wasu muhimman abubuwan da ya kamata ace an yi irin su bikin ranar ‘yancin kasar.
Wannan wuta tasa an kwashe mutane da yawa daga gidanjensu saboda ana tsammanin zata kai garesu.
Jiragen yakin kasar Israela na ta shawagi a sararin samaniyar kasar inda suke kokarin kashe wutar data tashi.
Hakanan bayan wutar, an kuma samu wata guguwa me karfi wadda take cike da yashi sosai ta taso a kasar ta Israela.
Rahotanni sun ce guguwar bata bari mutane na gani da kyau, sannan kuma tana kara rura wutar dajin.
Wannan Bidiyon na sama guguwar ce a yayin da take kara mamaye kasar.
Wasu sun bayyana wannan lamari da cewa fushin Allah ne ya fadawa kasar ta Israela lura da rashin imanin da take nunawa wajan kisan Falasdinawa.