
An samu wani shakiyyi ya hada hoton Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana rera wakar Hamisu Breaker ta Amanata wadda Hisbah ta jihar Kano ta Haramta Sauraro.
Da yawa sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi akan hakan.
Wakar dai ta samu watsuwa sosai fiye da yanda ake tsamani bayan haramcin Hisbah.