
Mutane da yawa ne a Kano ke tururuwa zuwa Hotoron Arewa inda suka ce an ga wani Gulbi a garin da sahun Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a cikinsa.
Mutane dai na kokawar shan ruwan da kuma yin wanka a cikinsa dan neman tubarraki.
Mutane sun mayar da gurin kamar wani wajan Ibada inda masu fama da ciwuka da suka dade basu warke ba ke zuwa dan su sha ruwan gulbin ko su yi wanka dashi.
A Bidiyon da ya watsu sosai a kafafen sadarwa wanda hutudole.com ya gani, an nuna yara da matasa maza da mata suna kokawar shan ruwan da watsawa a jikinsu.
A wajan an ga yanda Aljanun wata mata ya tashi sannan an ga yanda wata mata ko lullubi babu ta je wajan.