Tuesday, November 18
Shadow

Fastocin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 na gwamna Bala Muhammad sun cika Titunan Bauchi

An wayi garin yau, Litinin da fastocin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 na Gwamna Bala Muhammad a titunan Bauchi.

Rahoton yace an kika fastocin a guraren da suka fi faukar hankali irin su shataletale da jikin pol din wutar lantarki da sauransu.

Masu lika fastar sun ce wasu ‘yan siyasa Ya’u Ortega da Talolo ne suka basu aikin lika fastar.

Daily Trust ta yi kokarin jin ta bakin wadanda suka bayar da aikin lika fastar amma abin ya ci Tura.

Karanta Wannan  Dalibai a jami'ar Maradi University dake kasar Nijar sun Rhushye Katangar da aka gina dan raba bangaren maza dana mata a jami'ar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *