
Rahotanni sun bayyana cewa, Tauraruwar fina-finan Hausa, Fatima Kinal ta baiwa Ummi Nuhu Kayatar Naira Miliyan 1.
Hakan na zuwane bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi da Ummi Nuhu inda aka ganta cikin wani hali na tausayawa.
Mutane da yawa ne suka wallafa bayanan baiwa Ummi Nuhu da Kinal ta yi Naira Miliyan 1 inda suke wa Kinal addu’ar fatan Alheri.
A jiya ma dai, Bashir Mai Shadda ya tabbatar da mutane daga ciki da wajen Kannywood har daga kasashen waje sai tallafawa Ummi Nuhu suke.