
Tauraruwar Tiktok, Babiana da a baya ta wallafa Bidiyo da take zargin mutanen Arewa musulmai da cin zarafinta saboda bayyanar Bidiyonta na batsa, a yanzu ta goge wancan Bidiyon.
Duk da cewa, ta bayar da hakuri, ta sake yin sabon Bidiyon inda ta sake bada hakuri tace kalmar musulman Arewa da ta yi amfani da ita bata dace ba.
Babiana tace, Wasu sun kirata su ji halin da take ciki inda wasu suka tara mata kudi.
A Bidiyon ta na farko dai ta nemi taimakon shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shahararrun ‘yan kudi, VDM da Tunde Ednut.