
Tauraron mawakin Najeriya, 2face Idibia ya rabu da matarsa, Annie wadda suka dade tare hadda yara inda a yanzu ya fara soyayya da ‘yar majalisar jihar Edo, Natasha Osawaru.
2face ya fito ya bayyanawa Duniya cewa yanzu wadda yake so kuma yake da burin aure itace Natasha Osawaru kuma kada mutane su zargeta da cewa itace silar rabuwarsa da matarsa.
Bisa Al’adar mutanen kudu, 2face ya nemi Natasha ta aureshi kuma tuni ta amince masa da hakan.
Tuni 2face ya baiwa Natasha Zoben Alkawari
Lamarin da ya jawo cece-kuce sosaia kafafen sada zumunta.