Wannan wata ‘yar Najeriya ce a Dubai data dauki hankula bayan da ta bayyana abinda ya faru tsakaninta da wani Balarabe.
Ta dauki Balaraben Bidiyon inda yake tambayarta nawa zai bata(yayi Lalata da ita) amma sai tace masa Astagfirullah.
Cikin jin kunya ya juya.
Abin takaicin shine lamarin ya farune akan titi.
Saidai da yawan masu sharhi sun bayyana cewa akwai matan Najeriya da yawa da abinda ke kaisu Dubai din kenan shiyasa duka ake musu irin wannan kallon.