
Na hannun damar Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin, Watau Mustin Bestie ya bayyana cewa, abinda Gfresh din yake baya cikin hayyacinsa.
Ya bayyana cewa, tabbas Gfresh Al-amin ya saki matarsa.
A baya dai Hutudole ya kawo muku rahoton cewa, Gfresh ya saki matarsa inda ta tabbatar da hakan har take cewa Allah ya bata miji na gari.
Mistin Bestie yace Gfresh na da laifi amma matarsa, Maryam ta fishi laifi tunda ta kasa Danne zuciyarta kan abinda tasan halinsa ne.