
A yayin da wasan Senegal da Morocco na jiya ya kusa zuwa karshe, An baiwa Morocco bugun daga kai sai me tsaron gida wanda baiwa ‘yan wasan Senegal dadi ba.
Hakan yasa ‘yan wasan Senegal suka fita daga filin a matsayin wata hanya ta nuna fushinsu.
Saidai Kyaftin dinsu, Sadio Mane ya tsaya inda ya rika kiransu su dawo cikin fili a ci gaba da wasa, hakan ya jawo masa yabo sosai.
Kuma bayan dawowarsu sai suka sakawa Morocco kwallo 1 wadda hakan ya basu nasarar daukar kofin.