
Rahotanni daga jihar Ekiti na cewa, hukumar ‘yansandan jihar sun kama wani Fasto me suna Adegoke Adewuyi wanda ya kama otal ya biye yayi karyar wai an yi garkuwa dashi.
Faston ya hada baki da wasu inda ya nemi mabiyansa su hada Naira Miliyan 3 a matsayin kudin fansa dan a karboshi.
Saidai dubunsu ta cika inda aka kamasu su duka.