
An kammala horaswa da kuma yaye jami’an hukumar KOSSAP da aka samar na musamman a jihar Kano da zasu rika yaki da kwacen waya.
Jami’an su 380 an kammala yaye su ne a ranar Lahadi inda kuma zasu fara aiki nan ba da jimawa ba.
An shafe sati biyu ana basu horo.
Matsalar kwacen waya yayi kamari a jihar Kano inda ake kashe mutane ana kwace musu wayoyi.