
Tauraron Tiktok, Maiwushirya ya kwanta rashin lafiya kwana daya bayan da aka ce a daura masa aure da wada wadda aka fi sani da ‘YarGuda da suke Bidiyo da ita.
An ga dai ana masa karin ruwa yayin da yake kwance akan gado.
Wasu sun rika masa fatan samun sauki inda wasu ke cewa zullumin auren wada ne ya sashi gaba.