Friday, July 17
Shadow

Gwamnati ta kwace gidan dala Miliyan $2.5 da tsohon ma’aikacin kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Iheanacho Okoronkwo ya siya da kudin sata a kasar Amurka

Gwamnatin tarayya ta kwace gidan Dala Miliyan $2.5 da tsohon ma’aikacin kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Iheanacho Okoronkwo ya siya a kasar Amurka da kudin sata.

A watan Augusta ne aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan samunsa da laifin rashawa da cin hanci.

An sameshi da laifin karbar cin hanci har dala Miliyan $2.1 daga wani kamfanin mai me suna Addax Petroleum da zummar cewa zai samarwa da kamfanin lasisin hakar danyen man fetur a Najeriya.

Kuma ya sayi gidanne a Valencia dake California kasar Amurka.

Karanta Wannan  Biyo bayan nuna goyon baya ga Trump da goyon bayan Shi ya kawo Khàrì Najeriya, Fitsararriyar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj ta rasa mabiya Miliyan 4 a shafinta na sada zumunta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *