
Idris Maiwushirya ya bayyana bacin ransa kan abinda yace Abba EL-Mustapha ya masa inda yace ya shirya abinshi amma saboda bakin ciki aka sa yayi sarar Naira Miliyan 3.
Maiwushirya yace Abba El-Mustapha bai isa yasa a masa auren dole be sannan kuma shi da ya kama Chairlady a ni sai ka goyani wa yace sai ya aureta?
Ya kuma bayyana magungunan da ya saya saboda rashin lafiyar da ya kwanta duk saboda wannan matsalar.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya watsu sosai inda aka ganshi a kwance.
Ya kara da cewa da yana so ya auri ‘YarGuda ai da ba sai an tursasa shi ba.