Friday, July 17
Shadow

Ba zan tsaya takara a shekarar 2027 ba, na hakura haka, a samu wani matashi da bai kaini Shekaru ba shima ya zo ya gwada>>Inji Dan majalisar wakilai daga jihar Sokoto, Hon. Abdussamad Dasuki

Dan majalisar Wakilai, Hon. Abdussamad Dasuki me wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal daga jihar Sokoto ya bayyana cewa ba zai tsaya takara a shekarar 2027 ba.

Yace ya barwa matasa ‘yan kasa da shekaru 40 su tsaya takarar dan kawo sauyi da ci gaba a mazabar tashi.

Yace yayi hakanne ba dan ya gaji ko gazawa ba inda yace har yanzu shi matashi ne amma ya haura shekaru 40.

Yayi godiya ga mutanen mazabatarsa da iyayen gidansa a siyasa da suka bashi dama a shekaru 14 da yayi yana siyasar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Kwankwaso ya bayyana cewa suna magana da wata jam'iyyar da yake son komawa amma ya saka musu sharadin sai sun bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *